Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IMF da bankin duniya za su taimakawa kasashen duniya don shawo kan annobar COVID-19
2020-03-03 12:27:25        cri

Asusun ba da lamini na duniya (IMF) da bankin duniya sun ce a shirye suke su tallafawa kasashen duniya domin dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19 dake yiwa bil adama barazana da haifar da mummunan kalubale ga tattalin arziki. Manyan hukumomin biyu na kasa da kasa sun bayyana hakan ne a jiya Litinin cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar.

Sanarwar ta ce hukumomin biyu a shirye suke su yi aiki tare da cibiyoyin kasa da kasa, da hukumomin kasashen duniya, musamman wajen ba da fifiko ga kasashen duniya masu karancin wadata wadanda tsarin kiwon lafiyarsu ba shi da inganci, kana mutanen kasashen ba su da galihu.

A cewar sanarwar, cibiyoyin biyu za su yi iyakar kokarinsu gwargwadon hali, wajen taimakawa kasashen ta bangarori daban daban da suka hada da, samar da kudaden ayyukan gaggawa, da bayar da shawarwari, da tallafin kwararru. Musamman wajen samar da kudaden da ake bukata cikin gaggawa, don taimakawa kasashen wajen tinkarar matsalolin idan bukatar hakan ta taso. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China