Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Za a iya koyon fasahar dakile cutar COVID-19 da kasar Sin ta samu
2020-03-11 12:16:30        cri

Jiya Talata, Sin da hukumar kiwo lafiya ta duniya WHO sun kulla wata yarjejeniyar ba da tallafi, inda gwamnatin Sin ta baiwa WHO tallafin kudi dala miliyan 20 don taimakawa kasashen da ba su da karfin tinkarar cutar.

Bayan kulla wannan yarjejeniya, babban darektan hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yaba taimakon da Sin ta baiwa sauran kasashe masu tasowa a wannan lokacin da take kuma cikin mawuyacin hali, a daidai wannan lokacin da duniya ke fuskantar wannan annoba mai tsanani.

Yayin da yake amsa tambayoyin da wakilin CMG ya gabatar masa, Tedros ya ce, fasahar kasar Sin ta yi tasiri wajen dakile wannan sabuwar cuta. Yanayin fama da cutar a kasar Sin ya samu sauki, har an ci nasarar hana yaduwarta, kuma ana kokarin samar da allurar rigakafi. Duk wadannan sakamakon da take samu na da alaka sosai da jagorancin gwamnatin kasar, da kuma hadin kan jama'ar kasar Sin baki daya. Ya ce, wadannan bangarori biyu na da muhimmanci sosai wajen yakar cutar, idan sauran kasashe na iya daukar matakan kamar yadda Sin take yi, za a iya hana yaduwar annobar. Ya kuma kara da cewa, Sin ta riga ta dauki matakai da dama a duk fadin kasar gaba daya, ya kamata sauran kasashen duniya su yi amfani da wannan zarafi mai kyau don dakile annobar ba tare da bata lokaci ba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China