Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Donald Trump: kila tattalin arzikin Amurka na samun koma-baya
2020-03-17 13:11:34        cri

Jiya Litinin 16 ga wata, alkaluman "the Dow Jones Industrial Average" wato DJIA, sun fadi da kusan kaso 13 bisa dari, faduwar da ita ce mafi muni cikin shekaru 30. Dukkanin alkaluman 3 ba su samu wata kariya ba, kasancewar bude kasuwanni bai hana darajarsu ci gaba da sauka ba.

A daya hannun kuma, kasuwannin hannayen jari na Asiya da yankunan tekun Fasifik, sun kare cikin hasara, yayin da hannayen jarin Turai suka gamu da manyan asarori, kuma alkaluman farashin danyen mai 2 suka yi gagarumar faduwa.

Shugaba Donald Trump na kasar Amurka, ya bayyana a yayin taron manema labaru a fadar gwamnati wato White House cewa, kila za a yi yaki da yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 har zuwa watan Agustan bana. Ya kuma bukaci Amurkawa da su kaucewa yin taruwa tsakanin mutane 10 ko fiye da haka nan da kwanaki 15 masu zuwa, su kuma kaucewa cin abinci a dakin cin abinci, su kaucewa ziyartar abokai. Ya yi nuni da cewa, kila tattalin arzikin kasar zai samu koma-baya. Wannan shi ne karo na farko da ya ambato illolin da annobar za ta haifar. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China