![]() |
|
2020-03-04 10:59:52 cri |
A ranar 3 ga wata, asusun adana kudaden gwamnatin tarayyar Amurka ya sanar da rage kudin ruwa cikin gaggawa bisa maki 50 da kashi 1% -1.25% da nufin kawar da mummunar illar da annobar cutar numfashi ta COVID-19 za ta haifar wa tattalin arzikin kasar. Wannan shi ne ragewa mafi girma na kudin ruwa da ta yi tun bayan rikicin tattalin arziki da aka abku a shekarar 2008.
To sai dai kuma, rage yawan kudin ruwan bai kawar da fargabar da ake da shi na fuskantar tafiyar hawainiyar karuwar tattalin arzikin kasar a sakamakon barkewar annobar ta COVID-19 ba. A wannan rana kuma, kasuwar hannayen jarin kasar Amurka ta fuskanci matsanancin rashin tabbas. Inda kamfanin The Dow Jones ya fadi da maki 788. Masu zuba jari sun sayi bashin kasa ta Amurka da yawa, kana farashin zinare shi ma ya yi tashin gwauron zabi. (Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China