Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump ya ayyana matakin gaggawa kan amfani da asusun agaji na kasar wajen dakile COVID-19
2020-03-14 16:39:48        cri
Shugaban Amurka Donald Trump, ya ayyana matakin gaggawa kan amfani da dala biliyan 50 na asusun agaji na kasar, wajen dakile yaduwar cutar COVID-19.

Donald Trump ya ce ya ba sakataren harkokin lafiya da hidimtawa jama'a na kasar, ikon dage wasu dokoki da ka'idoji, da nufin tabbatar da dakile cutar COVID-19 tare da kula da marasa lafiya.

Ya kara da cewa, yana umartar dukkan jihohin kasar su kafa cibiyoyin ayyukan gaggawa domin taimaka musu yaki da cutar.

A cewar cibiyar nazarin tsarukan kimiyya da aikin injiniya ta jami'ar Johns Hopkins ta kasar, ya zuwa ranar Alhamis, Amurka ta bayar da rahoton samun mutane 1,663 da suka kamu da cutar COVID-19, inda a kalla mutane 40 suka mutu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China