Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban CDC na Amurka: Akwai wasu "masu ciwon Marisuwa" da ya yiwu suka mutu a sanadin cutar Covid-19
2020-03-12 16:27:49        cri
A yayin taron sauraron ra'ayoyin al'umma da majalisar wakilan kasar Amurka ta kira a jiya Laraba, wani dan majalisar da ya yiwa shugaban cibiyar shawo kan cututtuka ta kasar (CDC) Robert Redfield tambaya dangane da yadda ake fama da karancin kayayyakin gwajin cutar Covid-19 a kasar, inda ya ce daga cikin wadanda ake zaton sun mutu a sanadin cutar Marisuwa a kasar, (wato influenza a Turance) ko akwai wasu da ya yiwu sun mutu ne a sakamakon cutar Covid-19? Mr.Redfield ya amsa cewa, a hakika, akwai wadanda aka yi zaton sun kamu da cutar Marisuwa, amma sun mutu ne a sakamakon cutar Covid-19.

Wani rahoton baya-bayan da cibiyar shawo kan cututtuka ta Amurka ta fitar ya yi hasashen cewa, ya zuwa yanzu, akwai mutane kimanin miliyan 34 da suka harbu da cutar Marisuwa, kuma akwai wasu dubu 350 da suka kwanta a asibiti. Baya ga haka, Amurkawa kimanin dubu 20 sun mutu a sanadin cutar, ciki har da yara 136. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China