![]() |
|
2020-03-13 11:58:31 cri |
A jiya ne mizanin DJIA, wato Dow Jones Industrial Average, ya ragu da maki 2352 wanda ya ragu da kusan kaso 10, raguwar da ta fi muni a tarihi. Kana, sauran muhimman mizanai biyu, wato S&P 500 da NASDAQ, duk sun ragu da kusan kaso 10.
Ban da kasuwannin hannayen jari, farashin zinari da na mai duk sun ragu a duniya.
Duba da babbar faduwar darajar hannayen jarin Amurka, kasuwannin hannayen jarin kasashe daban-daban sun dakatar da ayyukansu don kaucewa hadari.(Murtala Zhang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China