Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafar watsa labaru ta Amurka: Amurka ta goyi bayan Kungiyar Uyghur ta Duniya don gudanar da ayyukan yaki da kasar Sin
2020-03-17 13:09:52        cri

A kwanakin baya, tashar internet ta kasar Amurka mai zaman kanta ta Grayzone ta gabatar da wani bayani, mai taken "Kungiyar Uyghur ta Duniya kungiya mai ra'ayin rikau ce da Amurka ke goyon baya wajen neman sauya mulkin siyasa na kasar Sin", inda aka bayyana cewa, a idanun jama'a, kungiyar Uyghur ta duniya kungiya ce ta kare hakkin dan Adam, amma tun da aka kafa ta, tana karkashin inuwar asusun demokuradiyya na kasar Amurka wato NED, bisa manufar gudanar da ayyukan kawo baraka ga kasar Sin.

Bayanin ya yi nuni da cewa, Kungiyar Uyghur ta duniya wadda ke da matsuguni a birnin Munich dake kasar Jamus, da kuma rassa 33 a kasashe da yankuna 18 na duniya, wata muhimmiyar hukuma ce ta Amurka na yin yakin cacar baka da kasar Sin bisa sabon salo. Asusun NED yana amfani da kudin harajin fiye da dala miliyan daya da Amurkawa ke biya a ko wace shekara wajen nuna goyon baya ga jam'iyyun adawa, da kungiyoyi masu zaman kansu, da suke da yunkurin hambarar da mulkin siyasar kasashensu. Kuma tun daga shekarar 2016 zuwa yanzu, asusun ya samar da kudi dala miliyan 1 da dubu 284 ga kungiyar Uyghur ta Duniya, baya ga samar da kudi fiye da dala miliyoyi da dama ga rassanta. Kana zakila ma, wadannan kungiyoyin adawa da kasar Sin, sun yi hadin gwiwa tare da wasu kafofin watsa labaru kamar gidan rediyon Free Asia, don samar da sauki ga kungiyar da wasu kafofin watsa labaran kasashen yammacin duniya masu kin kasar Sin wajen watsa jita-jita game da yankin Xinjiang. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China