Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mizanin DJIA na Amurka ya yi kasa sosai karon farko tun bayan barkewar rikicin hada-hadar kudi a shekara ta 2008
2020-03-10 13:12:55        cri

Wasu muhimman mizanai uku na hannayen jarin Amurka sun dagule matuka jiya Litinin, ciki har da mizanin DJIA, wato Dow Jones Industrial Average, wanda ya ragu da kaso 7.29 da yawansa ya wuce maki 2000, irin raguwar da ta kai matsayin koli tun bayan barkewar rikicin hada-hadar kudi a duniya a shekara ta 2008.

Raguwar darajar hannayen jarin Amurka na haifar da faduwar darajar hannayen jari a nahiyar Turai da sauran wasu kasashe da yankuna.

Rahotannin sun nuna cewa, "yakin farashi" da ake yi a kasuwar danyen mai, shi ne babban musabbabin raguwar manyan mizanan hannayen jarin uku a Amurka. Tuni a ranar 6 ga wata, aka rabu baram-baram a wajen shawarwarin kungiyar OPEC, daga baya wato ranar 7 ga wata, kasar Saudiyya ta rage farashin man fetur sosai, babbar raguwar da ba'a taba ganin irinta ba a shekaru 20 da suka wuce.

Manazarta na ganin cewa, yakin farashin da ake a kasuwar danyen mai ya ya zama dalili mafi girma dake matsa lamba ga kasuwannin hannayen jarin duniya maimakon cutar numfashi ta COVID-19. Kana suna damuwa sosai ga tattalin arzikin Amurka na yanzu da makomarsa nan gaba, kuma rashin sanin tabbas dake tattare da makomar tattalin arzikin Amurka ya sa darajar hannayen jarin kasar ta ragu kwarai da gaske.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China