Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Amurka da kungiyar Taliban za su kulla yarjejeniyar shimfida zaman lafiya tsakaninsu a yau
2020-02-29 16:30:20        cri
Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo zai halarci taron rattaba hannu kan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Amurka da kungiyar Taliban, wanda ake sa ran zai wakana yau Asabar a Doha, babban birnin kasar Qatar.

Cikin wata sanarwa da fadar White House ta fitar a jiya, Shugaba Trump ya ce idan kungiyar Taliban da gwamnatin Afghanistan suka cika alkawarinsu, za a samu gagarumin ci gaba wajen ingiza kawo karshen yaki a Afghanistan, tare da mayar da sojin Amurka gida.

Shugaba Trump ya kara da cewa, sakataren tsaron Amurka Mark Esper, zai fitar da wata sanarwar hadin gwiwa da gwamnatin Afghanistan, sai dai bai yi karin bayani game da kunshin sanarwar ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China