Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar 'yan jarida ta Sin ta yi tir da matakin Amurka na takaita yawan 'yan jarida Sinawa dake aiki a kasar
2020-03-06 14:46:07        cri
Kungiyar 'yan jarida ta Sin, ta yi tir, da Allah wadai da kiran da mahukuntan kasar Amurka suka yi, na takaita yawan 'yan jarida Sinawa dake aiki a Amurkan.

Kungiyar wadda ta zargi matakin da Amurka ta dauka na takaita yawan Sinawa 'yan jarida dake aiki a kasar, ta ce wannan mataki ya yi matukar sabawa 'yancin halas, da manufofin aiki da 'yan jarida Sinawa ke bi wajen aiwatar da ayyukan su a ketare. Kaza lika hakan ya bata sunan kafofin watsa labarai na kasar Sin, da 'yan jaridar kasar, ya kuma gurgunta yanayin aikin su a ketare. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China