Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta nuna kin amincewa da kasashen dake zargin Sin kan batun yankin Xinjiang ba tare da tushe ba
2020-02-27 10:51:00        cri

Zaunannen wakilin Sin a ofishin MDD dake birnin Geneva da sauran hukumomin duniya dake kasar Switzerland Chen Xu ya bayyana a gun muhawarar taron koli na 43 na majalisar hakkin dan Adam ta MDD cewa, Sin ta nuna kin amincewa ga wasu kasashe dake zargi kasar Sin kan batun yankin Xinjiang ba tare da tushe ba a gun taron kolin.

Chen Xu ya bayyana cewa, Sin ta dauki matakan yaki da ta'addanci da kawar da tsattsauran ra'ayi a yankin Xinjiang, ciki har da kafa cibiyar ba da horo da limin sana'oi da sauransu, wadanda suka kyautata yanayin kiyaye tsaron yankin Xinjiang, da tabbatar da hakkin dan Adam na jama'ar kabilu daban daban na yankin, kana da samar da muhimmiyar gudummawa wajen yaki da ta'addanci da kawar da tsattsauran ra'ayi a duniya baki daya. Ba a samu ayyukan ta'addanci ba har na tsawon shekaru fiye da 3 a yankin Xinjiang, kana dukkan masu karatu a cibiyar ba da horo da limin sana'oi sun gama karatunsu, da samun aikin yi tare da komawa harkokin zamantakewar al'umma bisa taimakon gwamnati, kuma zaman rayuwarsu ya kara samun kyautatuwa.

Chen Xu ya kara da cewa, Sin ta mayar da jin dadin zaman rayuwar jama'a a matsayin batun hakkin dan Adam mafi muhimmanci, da bin hanyar tabbatar da hakkin dan Adam bisa halin da ake ciki. Sin ta samu nasarori da dama kan bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma da kuma tabbatar da hakkin dan Adam, jama'ar kabilu daban daban suna jin dadin zaman rayuwarsu da zama tare cikin lumana. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China