Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya tattauna da Sakatare Janar na MDD, yana mai kira ga kasashen duniya su dauki matakan yaki da COVID-19
2020-03-13 10:23:36        cri

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna a jiya, da Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ta wayar tarho, inda ya bukaci kasashen duniya su dauki matakan yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

Xi Jinping ya ce, matakai masu tsauri da kasar Sin ta dauka, sun sa kasar na samun nasara a ayyukan kandagarki da dakile yaduwar cutar, sannan harkokin rayuwa da na samar da kayayyaki na komawa yadda suke cikin sauri.

Ya ce a mataki na gaba, kasar Sin za ta dauki matakai kamar yadda ta yi da farko, kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba dangane da kokarinta na kandagarki da dakile yaduwar cutar, sannan za ta sa samu ci gaba wajen aiwatar da ayyukan raya dukkan fannonin tattalin arziki da zamantakewa.

Har ila yau, shugaba Xi Jinping, ya ce ba makawa, al'ummar Sinawa za ta shawo kan annobar COVID-19 kuma ta cimma burin da ta sanya gaba na samun ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.

Da yake tsokaci kan barkewar cutar a wasu kasashe a baya-bayan nan, ya ce yanayin abun damuwa ne, don haka ya bukaci kasashen duniya su gaggauta daukar mataki, tare da hada hannu wajen daukar matakan kandagarki da na dakile yaduwar cutar, domin hada karfi da karfe wajen shawo kanta.

Ya ce a shirye Sin take, ta bayyana dabarunta ga sauran kasashe, da gudanar da bincike cikin hadin gwiwa da samar da magani da rigakafi da kuma ba da taimako iya karfinta, ga kasashen da annobar ta barke.

Ya kara da cewa, kasar Sin na goyon bayan MDD da hukumar lafiya ta duniya WHO, a kokarin fadakar da kasashen duniya game da samar da dabaru da abubuwan da ake bukata da kuma taimakawa kasashe masu tasowa dake da tsarin kiwon lafiya mara inganci, wajen shiryawa daukar matakan kariya da tunkarar cutar.

Xi Jinping, ya ce kasar Sin ta sanar da bada gudunmuwar dala miliyan 20 domin taimakwa ayyukan WHO na tsara dabarun yaki da annobar a duniya. Yana mai cewa, annobar ta kara nuna yadda dukkan bil Adama ke da makoma iri daya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China