Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta tura tawagar kwararru da kayayakin lafiya zuwa Italiya
2020-03-13 10:33:04        cri

A jiya da dare ne, wani jirgin saman musamman da kasar Sin ta yi hayarsa, dauke da wata tawaga da ta kunshi ma'aikatan agaji Sinawa guda 9 da tan-tan na kayayyakin kiwon lafiya, ya isa filin jirgin sama na Fiumicino dake birnin Roma na kasar Italiya, a wani mataki na kokarin kasar Sin na taimakawa kasar Italiya yakar cutar COVID-19.

Hukumar lafiya ta kasar Sin da kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Sin ce suka shirya wannan tawaga. Kuma wannan ita ce tawagar masana ta uku da hukumomin kasar ta Sin suka tura zuwa kasashen ketare, bayan tawagogin da aka tura kasashen Iran da Iraki. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China