Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta fita daga kololuwar yaduwar COVID-19
2020-03-13 10:24:41        cri
Mai Magana da yawun hukumar lafiya ta kasar Sin Mi Feng, ya shaidawa taron manema labarai a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin cewa, kasar ta fita daga kololuwar barkewar cutar numfashi ta COVID-19, sa'o'i bayan da hukumar lafiya da duniya WHO a takaice, ta ayyana cutar a matsayin annobar da ta shafi duniya baki daya.

Wani kwararren kan fannin hanyoyin numfashi na kasar Sin, ya bayyana cewa, idan har kasashe da dama na duniya suka dauki managartan matakai kamar yadda kasar Sin ta yi, za a shawo kan cutar nan zuwa watan Yuni.

Bayanai na nuna cewa, a nan kasar Sin, ana ci gaba da samun raguwar sabbin mutane dake kamuwa da cutar, kuma baki dayan yanayin annobar na raguwa matuka.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China