Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na fadada hadin-gwiwa da kasa da kasa don yakar annobar COVID-19
2020-03-06 20:14:59        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yau Jumma'a cewa, a yayin da take ci gaba da kokarin ganin bayan annobar cutar numfashi ta COVID-19, Sin na fadada hadin-gwiwa da kasa da kasa ta hanyoyi daban-daban, domin ba su goyon-baya da tallafi gwargwadon karfinta.

Tuni, shugaban tawagar hadin-gwiwar kwararrun binciken cutar COVID-19 na Sin da hukumar WHO, Bruce Aylward ya jinjinawa managartan matakai gami da nasarorin da kasar Sin ta cimma ta fannin yakar cutar, inda a cewarsa, dabarun kasar Sin abubuwan misali ne, wadanda sauran kasashe za su iya yin koyi.

Zhao ya kara da cewa, kasar Sin na kara yin mu'amalar fasahohi tare da wasu kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da WHO, da EU, da AU, da CARICOM da kuma ASEAN, gami da wasu kasashe dake fuskantar babbar matsalar cutar ko masu raunin tsarin kiwon lafiya, ciki har da Koriya ta Kudu, da Iran, inda za'a iya musanyar ra'ayoyi da bayanai da kuma taimakawa juna ta fannin dabarun kandagarkin cutar.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China