Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta kyautata matsayinta cikin tsarin masana'antun duniya
2020-03-02 16:28:43        cri
Bayan barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, yawancin masana'antun da ke babban yankin kasar Sin sun dakatar da ayyukansu, wanda hakan ya sa aka dakatar da wasu tsare-tsaren masana'antu da samar da kaya a duniya. Wasu jami'an kasar Amurka sun yi kiran da a kafa sabon kawancen duniya, a yunkurin daina dogaro da tsarin samar da kaya na kasar Sin. Amma in an tantance abubuwan da suka faru bisa sanin ya kamata, za a gano cewa, illar da annobar ta haifar ta wucin gadi ce. Kasar Sin za ta kara inganta matsayinta cikin tsarin samar da kaya da na masana'antun duniya.

Kasar Sin ba kawai tana samar da kaya ba ne, har ma ta fi sauran sassa yin sayayya a duniya, lamarin da ya sa tsarin masana'antu, da na samar da kaya ba za su kaura zuwa sauran wuraren duniya ba sakamakon barkewar annobar ko yakin ciniki.

Muddin kasar Sin ta ci gaba da yin gyare-gyare a gida, da kara azama kan kyautata masana'antu, da hakaba bukatu a gida, da kyautata muhallin kasuwanci, hakan zai kara inganta matsayin ta cikin tsarin samar da kaya da na masana'antu a duniya.

Barkewar annobar ta dan dakatar da kokarin kasar Sin na kafa cikakken tsarin masana'antu. Nan gaba, ba shakka za a yi garambawul a wasu masana'antu na wasu wurare, amma kuma yawan sassan kamfanoni wadanda suke a mataki na koli da za su dawo da ayyukansu nan kasar Sin zai karu. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China