Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: A kara karfin yaki da annoba cikin hadin gwiwar kasa da kasa
2020-03-02 12:10:20        cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi bayani mai taken "samun nasarar yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19 tare da kara azama kan raya kyakkyawar makomar dan Adam ta bai daya" cikin Mujallar Qiushi, a jiya Lahadi, inda ya yi nuni da cewa, yaduwar annobar ta ilmantar da mutane cewa, a halin yanzu da ake raya duniya baki daya, ba a iya raba wata kasa daga sauran kasashe, domin ana shan wahala tare, a kuma ji dadin zama tare. Wang Yi ya ce, raya kyakkyawar makomar dan Adam ta bai daya, kyakkyawar manufa ce daya tilo da za a iya bi wajen samun ci gaban zaman al'ummar kasa.

A cikin bayaninsa, Wang Yi ya ce, kasar Sin za ta yi amfani da damar yaki da annobar cikin hadin gwiwa, wajen inganta hadin kan kasa da kasa, a kokarin kyautata duniya tare. Ya ce Kasar Sin za ta habaka hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban wajen yaki da annobar, kuma za ta ci gaba da tuntubar hukumar lafiya ta duniya WHO yadda ya kamata, za kuma ta dauki matakan kandagarki da dakile yaduwar annobar cikin hadin gwiwar kasa da kasa a iyakokinsu. Har ila yau, kasar Sin za ta sanar da bayanan annobar, matakan kandagarki da hana yaduwar annobar da sakamakon nazari kan lokaci. Kana za ta kara Karfin nazarin magani da allurar rigakafi cikin hadin gwiwar kasa da kasa. Haka zalika kasar Sin za ta taimakawa kasashe da yankunan da ake samun barkewar annobar gwargwadon karfinta, a kokarinta na taka rawa a matsayin babbar kasa mai sauke nauyinta. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China