Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Li Keqiang: ya kamata a kara kula da likitocin da suke ba da jinya ga masu fama da cutar COVID-19
2020-03-06 09:51:20        cri
A jiya ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya shugabanci taron rukunin shugabanni na tinkarar cutar COVID-19.

A gun taron, Li Keqiang ya yi nuni da cewa, ya kamata a bi jawabin shugaba Xi Jinping, da tunanin taron zaunannen kwamitin hukumar siyasa na tsakiya na JKS, da kuma bin bukatun rukunin shugabanni na tinkarar cutar COVID-19, da kiyaye daukar matakan magancewa, da yaki da cutar, da kara kula da likitocin da suke ba da jinya ga masu fama da cutar, da tabbatar da zaman rayuwar jama'a wadanda suke shan wahala a yayin tinkarar cutar, da mayar da ayyukan kamfanoni yadda ya kamata, don sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki, da zamantakewar al'umma.

Kana an saurari ayyukan da aka gudanar, wajen magancewa, da yaki da cutar a cikin kasar Sin, da kuma yanayin yaduwar ta a kasashen waje, da kyautata matakan magancewa, da yaki da cutar bisa yanayin yankunan da ke ciki, da ci gaba da maida birnin Wuhan, da lardin Hubei a matsayin wurare mafiya muhimmanci, da yin namijin kokarin ba da jinya ga wadanda suka kamu da cutar mai tsanani, da kara rage yawan mutanen da suke mutuwa a sakamakon cutar, da kuma kara yawan mutanen da suka samu sauki. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China