Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanoni mallakar gwamnatin Sin sun dawo bakin aiki, a kokarin aiwatar da yarjejeniyoyin duniya
2020-03-02 12:13:35        cri

Kamfanoni mallakar gwamnatin kasar Sin, wadanda suke taka muhimmiyar rawa a fannin samar da kayayyaki a duniya, suna kandagarki da dakile yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19, tare da daukar mabambantan matakan tabbatar da gudanar da ayyukan kasa da kasa yadda ya kamata. Sun kuma kara karfin hada kai da kamfanonin kasa da kasa, a kokarin aiwatar da yarjejeniyoyin kasa da kasa kan lokaci, kuma bisa tanade-tanaden da ke cikin yarjejeniyoyin, lamarin da ya nuna aniya da karfin kamfanonin kasar Sin na cika alkawari.

Rahotanni sun ce, yawan kamfanoni mallakar gwamnatin kasar, da kuma rassansu da suka dawo bakin aiki ya zarce kashi 90 cikin kashi dari bisa jimillarsu, adadin ya kai har kashi 100 cikin dari a wasu sana'o'in.

Yayin da ake yaki da annobar a sassa daban daban na kasar, ana daukar matakai da dama, don tabbatar da ganin ma'aikata sun dawo bakin aiki yadda ya kamata, kana kamfanoni sun dawo baki aiki, an kuma ci gaba da gudanar da manyan ayyukan. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China