![]() |
|
2020-03-11 09:55:00 cri |
Ministan lafiya na kasar, Eteni Longondo, ya tabbatar da samun bullar cutar na farko ne a jiya, daga wani bako da ya je kasar daga kasar Belgium, wanda kuma aka duba lafiyarsa da isarsa Jamhuriyar ta Congo.
A cewar cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Tarayyar Afrika, baya ga bullar cutar da aka samu a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, an samu mutane 102 da suka kamu da cutar a kasashen nahiyar 10, inda mutum 1 ya mutu.
A ranar Litinin ne Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya kafa wani kwamitin ko-ta-kwana, domin taimaka wajen dakile yaduwar cutar a kasar, wadda ke da mutane biyu da suka kamu da cutar.
Sanarwar da ya fitar, ta ce, matakin yunkuri ne na shiryawa tunkarar yiwuwar barkewar cutar a kasar, wanda zai bukaci dabaru daga bangarori da hukumomin gwamnati daban-daban, kamar yadda WHO ta bada shawara, kamar dai yadda aka yi a lokacin annobar cutar kanjamau shekaru 20 da suka gabata.
Da yake jawabi ga wani taron manema labarai jiya a hedkwatar AU dake Addis Ababa na Habasha, daraktan cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Afrika, John Nkengasong, ya ce cibiyar ta kara karfinta na shiryawa tunkarar barkewar cutar COVID-19 da kuma kai dauki ga kasashen nahiyar. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China