Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Najeriya: COVID 19 ba ta illata tattalin arzikin duniya sosai ba saboda gudunmawar da JKS ta kasar Sin ke bayarwa
2020-03-11 12:12:35        cri

Jiya Talata, darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin dake Najeriya Charles Onunaiju ya wallafa wani bayani mai taken "Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS da lokacin bayan shawo kan cutar COVID 19" da ya rubuta a jaridun "Blueprint" da "People's Daily" da sauran jaridun kasar, inda ya yaba kokarin da jama'ar kasar Sin suke yi wajen dakile wannan cutar da kuma dawo da ayyukan samar da kayayyaki da harkokin rayuwar jama'a bisa jagorancin JKS, inda ya yi kira ga kasashen Afrika da su karfafa alakarsu da kasar Sin don samun ci gaba tare.

A cikin bayanin nasa, ya nuna cewa, tun bullowar wannan cutar, Sin ta dauki matakai masu inganci na hana yaduwar wannan cuta cikin watanni biyu kacal, har aka maido da ayyukan samar da kayayyaki da harkokin zaman rayuwar jama'a, matakin da ya taimakawa tattalin arzikin duniya rashin fadawa cikin hali na rashin tabbas. An samu wadannan nasarori bisa jagorancin JKS. Sakamako mai kyau da kasar Sin ta samu wajen dakile wannan cuta, na da alaka matuka da tunanin hanyar tsarin mulki na gurguzu mai sigar musamman a sabon zamani da ake ciki, matakin da ya baiwa duk duniya gudunmawa mai inganci sosai wajen yaki da cutar.

Ban da wannan kuma, Onunaiju ya ce, JKS ta yi alkawari ga jama'a cewa, za a kawar da kangin talauci gaba daya a dukkan kauyukan kasar Sin kafin karshen shekarar 2020 bisa mizanin da aka tsayar yanzu, don haka, kamata ya yi kasashen Afrika su koyi darasi daga kasar Sin a wannan fanni, tare da karfafa hadin kai da kasar Sin da kuma yin amfani da damar cika shekaru 20 da kafuwar dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika, ta yadda za su magance matsalolin fama da talauci, da yunwa dake addabar nahiyar, don kara samun nasara da ingiza bunkasuwar nahiyar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China