Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Nijeriya: yadda kasar Sin take yaki da annoba ba tare da rufa-rufa ba ya ilmantar da mutane
2020-03-06 13:20:30        cri
Kwanan baya, shehun malami Joseph Golwa, mataimakin shugaban cibiyar nazarin zaman lafiya da rikici a Tarayyar Nijeriya, ya rubuta wani sharhi mai taken" yadda kasar Sin ke yaki da annoba ba tare da rufa-rufa ba ya ilmantar da mutane" cikin wasu manyan kafofin yada labaru na kasar, kamar jaridar the Sun, inda ya jinjinawa kokarin da kasar Sin take yi, wajen dakile yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19, da kuma abubuwan da ta sadaukar da su.

A ganinsa, kasar Sin ta ba da jagoranci wajen raya kyakkyawar makomar bai daya ta bil'Adama, da aiwatar da "shawarar ziri daya da hanya daya". Masanin ya kuma yi kira ga kasashen duniya, da su yi koyi da fasahohin kasar Sin wajen dakile yaduwar annobar.

Golwa ya bayyana cikin sharhinsa cewa, gwamnatin kasar Sin da jama'ar kasar, sun dauki matakai masu karfi nan take ba tare da bata lokaci ba wajen yaki da annobar, lamarin da ya dakatar da yaduwar annobar a duk duniya.

Ya ce annobar tana yaduwa a ketaren kasa da kasa. Yadda aka zargi kasar Sin dangane da barkewar annobar babu dalili. Babu wata kasa wadda za ta iya kare kanta daga yaduwar annoba. Kana kuma bai kamata a sanya siyasa kan batun dakile yaduwar annobar ba. Ana kuma bukatar hada kai wajen dakile yaduwar ta. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China