Mutane 7169 daga kasashe 58 a wajen kasar Sin sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19
Hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa WHO, ta gabatar da sabon rahotonta jiya 1 ga watan Maris, game da yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19, wanda take gabatarwa a ko wace rana, inda ta ce, ya zuwa karfe 10 na safiyar ranar 1 ga watan, mutane 7169 daga kasashe 58, a wajen kasar Sin sun kamu da annobar, ciki had da wasu 104 da suka rasa rayukansu sakamakon annobar.
An samu sabbin mutane 1160 da suka kamu da annobar a wajen kasar Sin, a ranar 1 ga wata, wadanda suka fito daga kasashen Azerbaijan, Ecuador, Ireland, Monaco, da Qatar. (Tasallah Yuan)