Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Asusun MDD ya ware dala miliyan 15 don tallafawa kasashen duniya yaki da COVID-19
2020-03-02 11:15:29        cri
Ranar 1 ga watan Maris, asusun tallafin gaggawa na MDD ya ware dala miliyan 15 domin tallafawa ayyukan yaki da annoba cutar numfashi ta COVID-19 a kasashen duniya, musamman kasashen da tsarin kiwon lafiyarsu yake da rauni sosai.

A cewar MDDr, hukumar lafiyar ta duniya WHO, da asusun tallafawa kananan yara na MDD wato UNICEF, za su yi amfani da kudaden wajen gudanar da muhimman ayyuka, kamar gwaje gwajen hanyoyin yaduwar cutar, da yin bincike, da kuma gudanar da ayyuka a manyan dakunan gwaje gwaje na kasashen duniya.

Yiwuwar yaduwar kwayoyin cutar a kasashen da tsarin kiwon lafiyarsu ba shi da inganci shi ne babban abin fargaba da hukumar WHO ke nunawa. Dr. Tan Desai, darakta janar a hukumar WHO, ya ce ya yi maraba da ware kudaden. Shi kuwa Henrietta fall, shugaban asusun tallafawa kananan yara na MDD UNICEF, ya ce UNICEF za ta yi amfani da kudaden wajen taimakawa MDD don ilmantar da kananan yara da mata masu juna biyu da iyalai wajen samar musu da muhimman bayanai game da hanyoyi da za su kare kansu daga kamuwa daga cutar a duk fadin duniya. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China