2020-03-02 10:22:01 cri |
Kafar Press TV ta kasar ta rawaito wani jami'in hukumar birnin Yazd Mahmoud Dehqan, na cewa wannan mataki ya samu amincewa daga majalissar koli ta addinin musulunci dake kasar, kuma ana sa ran fara ginin asibitin tun daga karshen mako.
A cewar jami'in, burin mahukuntan kasar shi ne kammala aikin ginin wannan asibiti cikin kwanaki 3 masu zuwa. Bisa shirin da aka yi, asibitin mai fadin sakwaya mita 1,000, zai kunshi sashen kula da marasa lafiya na gaggawa, da dakin ajiye kayayyaki da ka iya kunsar kwayoyin halittu masu hadari ga lafiya.
A wani ci gaban kuma, mataimakin shugaban rundunar sojojin kasar mai lura da tsare tsare Habibollah Sayyari, ya ce rundunar ta ware wasu asibitoci guda 3 cike da kayayyakin aiki, musamman domin kula da masu fama da cutar ta COVID-19.
A jiya Lahadi ne kuma, ministan lafiyar kasar Iran ya sanar da cewa, yawan masu dauke da wannan cuta a kasar ya kai mutum 987, ta kuma hallaka mutane 54. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China