Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin sulhun MDD ya amince da kudurin goyon bayan yarjejeniyar sulhun Afghanistan
2020-03-11 10:11:52        cri
A ranar Talata kwamitin sulhun MDD ya amince da kudurin dake nuna goyon bayan ci gaban da aka samu na baya bayan nan game da batun yarjejeniyar zaman lafiyar kasar Afghanistan.

Kudurin mai lamba 2513, wanda ya samu amincewar dukkan mambobin kwamitin MDD 15, ya yi maraba da muhimman matakan da aka dauka na kawo karshen yaki da kuma bude kofar tattaunawar sulhu tsakanin bangarorin Afghanistan wanda ya baiwa bangarorin biyu damar sanya hannu kan yarjejeniyar tsakanin kasar Amurka da 'yan Taliban da kuma tsakanin kasar Amurka da gwamnatin kasar Afghanistan.

Kudurin ya kuma yi maraba da aniyar dukkan bangarorin kasar Afghanistan domin neman cimma nasarar daidaito da nufin warware takaddamar siyasa da tabbatar da cikakken shirin tsakaita bude wuta na dindindin.

Ya kuma jaddada muhimmancin shigar da mata, matasa, da kananan kabilu, kana ya tabbatar da cewa tilas ne duk wata yarjejeniyar siyasa ta tabbatar da kare hakkin dukkan 'yan kasar Afghanistan da mutunta muradun 'yan kasar domin samun dawwaumamman zaman lafiya mai dorewa. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China