Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban jami'in MDD ya yi Allah wadai da harin bam da aka kaddamar a wajen bikin aure a Kabul
2019-08-19 11:03:23        cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da harin bam da aka kaddamar kan fararen hula a daren ranar Asabar a birnin Kabul, babban birnin kasar Afghanistan.

A wata sanarwa da kakakin babban sakataren MDDr Stephane Dujarric ya fitar, mista Guterres, ya yi tir da mummunan harin ta'addancin na ranar 17 ga watan Agusta da aka kaddamar kan mahalarta bikin aure a Kabul, wanda ya yi sanadiyyar kashe rayukan mutane 63 da kuma jikkata wasu fiye da 180.

Babban jami'in MDD ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su da gwamnati da kuma al'ummar kasar Afghanistan.

Ya yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka samu raunuka.

Kungiya mai da'awar kafa daular Islama IS, ta dauki alhakin kaddamar da mummunan harin, kamar yadda wata kafar yada labaran kasar Afghanistan ta ba da rahoto. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China