Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Sin da Afghanistan da Pakistan sun cimma wata gagarumar matsaya dangane da batutuwan yanki da na hadin gwiwa
2019-09-08 17:16:01        cri
Kasashen Sin da Afghanistan da Pakistan, sun cimma wata gagarumar matsaya dangane da batun zaman lafiya a Afghanistan da dangantakarta da Pakistan da kuma hadin gwiwa tsakanin kasashen 3, yayin wani taron Ministocin harkokin wajen kasashen 3 da aka yi yau Lahadi, a birnin Islamabad na Pakistan.

A cewar mamban majalisar gudanrwar kasar Sin kuma Ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, kasashen 3 sun amince cewa, dangantaka tsakaninsu ya cimma nasararori ta fuskar kyautata warware matsalar siyasa a Afghanistan da inganta hadewar sassan yankin da kuma ci gaba na bai daya.

Bangarorin 3, sun amince da ingiza dangantakarsu karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, kana a shirye suke su inganta hadewa da juna, ta hanyar fadada zirin raya tattalin arziki da ke tsakanin Sin da Pakistan zuwa ga Afghanistan, da kuma hada hannu wajen gina babbar hanyar da za ta hada Kabul da Peshawar.

Bugu da kari, sun amince da aiwatar da ayyukan a bangarorin zaman takewa da tattalin arziki da karfafa musaya tsakanin jama'arsu. (fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China