Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wani abu ya fashe a kusa da ofishin jakadancin Amurka dake Kabul
2019-09-11 11:08:32        cri

Majiyoyi da dama sun ce an ji kara mai karfi na fashewar wani abu a kusa da ofishin jakadancin Amurka dake Kabul, babban birnin Afghanistan da sanyin safiyar yau Laraba.

Hotunan dake yawo a kafofin sada zumunta sun nuna yadda hayaki ke turnuke sama a kusa da ginin ofishin jakadancin Amurka dake wani kebattaccen yanki, inda sauran ofisoshin jakadancin kasashen waje suke a birnin Kabul.

Wani dan jarida na kasar, Jawad Jalali, ya ruwaito cewa an kai harin ne da makamin roka.

Kawo yanzu ba a bada rahoton aukuwar harin a hukumance ba, amma ana fargabar akwai wadanda lamarin ya rutsa da su. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China