Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin tsaron MDD ya yi Allah wadai da harin ta'addanci a Afghanistan
2019-09-20 13:52:47        cri
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fitar da wata sanarwa jiya Alhamis, inda ya la'anci wasu jerin hare-haren ta'addanci da aka kai a kasar Afghanistan kwanakin baya, tare da jajantawa iyalan mamatan gami da gwamnatin kasar.

Kwamitin tsaron ya jaddada cewa, duk wani nau'in ta'addanci mummunar barazana ce ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, ya kamata kasa da kasa su yi namijin kokarin shawo kan irin wannan barazana.

An kai harin bom da aka dasa a cikin wata mota a birnin Qalat na jihar Zabul dake kudancin kasar Afghanistan, lamarin da ya halaka mutane 15, tare da jikkata wasu 66. Ko da a ranar 17 ga wata ma, an kai wasu hare-hare a jihar Parwan dake gabashin kasar gami da birnin Kabul, inda mutane 46 suka gamu da ajalinsu. Kungiyar Taliban ta sanar da daukar alhakin kai wadannan hare-hare.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China