Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Trump ya kai ziyarar ba zata Afghanistan
2019-11-29 11:28:33        cri

Shugaban Amurka Donald Trump, ya gana da shugaban kasar Afghanistan Mohammad Ashraf Ghani, yayin zayarar ba zata da ya kai kasar a jiya Alhamis.

Rahotanni sun ce shugaban na Amurka ya gana da dakarun sojin kasar sa dake Afghanistan, inda ya taya su murnar zagayowar bikin "Thanksgiving" na mabiya addinin kirista.

Wannan ce ziyarar shugaba Trump ta farko a Afghanistan, tun bayan hawan sa kujerar shugabancin Amurka. Ya kuma shaidawa 'yan jaridu cewa, yayin zantawar sa da shugaban kasa Ashraf Ghani, sun tattauna game da muhimmin ci gaba da aka samu, karkashin ayyukan soji da sassan biyu suke gudanarwa, ciki hadda murkushe kungiyar Daesh ko IS, mai tada kayar baya a gabashin kasar ta Afghanistan.

Yayin ganawar shugabannin biyu da ta wakana a sansanin sojojin sama na Bagram, wanda shi ne babban sansani na hadin gwiwar dakarun kasashen biyu, mai nisan kilomita 50 arewa da birnin Kabul, sassan biyu sun amince cewa, muddin kungiyar Taliban na da burin kawo karshen tashin hankali, to ya zama dole ta amince da tsagaita bude wuta.

Cikin wani sakon Twitter da ya wallafa, shugaba Ghani ya ce, shugaba Trump ya jinjinawa kwazon dakarun tsaron Afghan dake fafatawa a fagen daga. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China