![]() |
|
2020-03-06 10:24:17 cri |
Wannan na zuwa ne bayan Ministan lafiya na kasar Zweli Mkhize, ya bayyana samun mutum na farko da ya kamu da cutar a kasar.
Ministan ya bayyana a jiya cewa, cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta kasar, ta ce sakamakon gwajin da aka yi wa wani da ake zaton na dauke da cutar, ya tabbtar ya kamu da ita, lamarin da ya sa kasar kara taka tsantsa.
Zweli Mkhize, ya ce mara lafiyan mai shekaru 38, ya je kasar Italiya tare da matarsa. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China