Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin dake Nijeriya ya bada bayani game da tasirin da cutar COVID-19 ke yiwa kasar Sin
2020-03-06 10:53:54        cri
A jiya ne, aka wallafa bayanin da jakadan Sin a Nijeriya Zhou Pingjian ya rubuta, mai taken "Cutar COVID-19 ta yi tasiri na gajeren lokaci ga tattalin arzikin Sin".

A cikin bayanin, an yi nuni da cewa, tun daga kafuwar sabuwar kasar Sin, cutar COVID-19, ta zama kalubalen kiwon lafiya da ta fi saurin yaduwa, a karin wurare daban daban, mai kuma wuyar yaki matuka. Bisa jagorancin shugaba Xi Jinping, Sin ta bi tunanin raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama, da yin kokarin yaki da cutar. Sin ta dauki alhakin kiyaye lafiyar jama'ar kasar ta, ta kuma taka rawa wajen tabbatar da kiwon lafiyar al'ummar duniya.

 

 

Gwamnatin kasar Sin, ta dauki matakan magancewa, da yaki da cutar a dukkan fannoni, yawancinsu sun zarce shawarar hukumar kiwon lafiya ta duniya, da kuma bukatun ka'idojin kiwon lafiya na duniya. Sin tana da karfi, da imani na cimma nasarar yaki da cutar, da cimma burin da aka tsara wajen bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'ummarta.

Babu shakka, cutar COVID-19 ta kawo kalubale ga bunkasar tattalin arziki, da zamantakewar al'ummar kasar Sin, amma tasirin ba zai kasance na dogon lokaci ba. Ana iya daidaita matsalar tattalin arziki da ake fuskanta a kasar Sin, kuma ba a samu koma baya a sakamakon cutar ba. Za a kiyaye samun bunkasuwar tattalin arziki, ba tare da canja abubuwan dake nuna goyon baya ga bunkasar tattalin arzikin Sin ba. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China