Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na fatan Amurka za ta mutunta tarihin dangantakar kasashen biyu bisa gaskiya
2020-02-11 19:48:41        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Geng Shuang, ya amsa tambayoyi a shafin yanar gizo na Intanet, inda ya ce kalaman da ministan harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya yi a kwanan baya, sun yi biris da tarihi, da kuma halin da ake ciki mai nasaba da dangantakar kasashen biyu, amma kuma duk abun da ya bayyana, na cike da tunanin yakin cacar baki, da kuma bambancin ra'ayi a siyasance. Don haka ko alama Sin ba za ta amince da kalaman nasa ba. Kuma Sin ta na gargadi ga Mr. Pompeo, cewa kamata ya yi ya yi watsi da wadannan ra'ayoyi marasa kyau, ya mutunta tarihin dangantakar kasashen biyu bisa gaskiya, sannan kuma da daina shafawa tsarin siyasar kasar Sin bakin fenti, da dakatar da daukar matakan illata hadin kan kasashen biyu.

A sa'i daya kuma, Geng ya jaddada cewa, Sin tana bin hanyar tsarin mulki mai halayen musamman na gurguzu, karkashin jagorancin jami'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Kaza lika jama'ar kasar Sin za su nace ga wannan hanya ba tare da tangarda ba, kuma za su samu ci gaba mai armashi nan gaba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China