Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Liu He ya gana da wasu manyan kusoshin kungiyar duniya da wakilan 'yan kasuwar Amurka
2020-01-16 09:33:33        cri

A safiyar ranar 14 ga wata bisa agogon Washington D.C., hedkwatar mulkin Amurka, mataimakin firaministan kasar Sin Liu He kana jagoran tawagar kasar Sin a tattaunawar tattalin arziki a tsakanin Sin da Amurka daga dukkan fannoni, bi da bi ya gana da shugabar asusun ba da lamunin duniya na IMF Kristalina Georgieva da shugaban kungiyar 'yan kasuwan Amurka Thomas Donohue da kuma shugaban kwamitin cinikayya a tsakanin Amurka da Sin na kasar Craig Allen.

Yayin ganawar Liu He ya bayyana cewa, IMF da kungiyar 'yan kasuwar Amurka da kwamitin cinikayya a tsakanin Amurka da Sin na kasar sun ba da gudummawa ga shawarwarin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka. Yadda bangarorin biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu a mataki na farko bisa tushen zaman daidai wa daida da girmama juna, zai amfana wa Sin da Amurka har ma da duniya baki daya. Wannan mataki ba ma kawai ya shafi fannin tattalin arziki da cinikayya ba, har ma zai taimaka wajen kiyaye zaman lafiya da na karko da samun wadatar duniya.

A nata bangaren, Madam Georgieva ta furta cewa, ta taya Sin da Amurka murnar daddale yarjejeniyar, a ganinta, matakin ya kara samar da kwanciyar hankali ga tattalin arzikin kasashen biyu har ma da na duniya. Asusun IMF ya riga ya daga hasashen da ya yi kan karuwar saurin tattalin arzikin Sin na shekarar 2020 daga kaso 5.8 zuwa 6.

Ban da haka kuma, Mr. Donohue da Mr. Allen sun furta cewa, yadda Amurka da Sin suka rattaba hannu a kan yarjejeniyar zai amfanawa kamfanoni da kasuwanni sosai.(Kande Gao)

 

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China