2020-01-16 12:55:42 cri |
Jiya Laraba, aka yi bikin kulla matakin farko na yarjejeniyar tattalin arziki da kasuwanci a tsakanin kasashen Sin da Amurka a fadar White House ta kasar Amurka. Wakilin ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS, mataimakin firaministan kasar Sin, kana, jagoran tawagar kasar Sin a shawarwarin tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka Liu He da shugaban kasar Amurka Donald Trump su ka rattaba hannu kan yarjejeniyar a hukumance.
Wakilan tattalin arziki da 'yan kasuwan kasar Amurka sun yi maraba matuka da kulla yarjejeniyar, suna ganin cewa, wannan yarjejeniyar za ta taimaka wajen cimma moriyar juna. Kana, wasu masana tattalin arziki da manyan jami'an gwamnatocin yankunan kasar Amurka sun nuna cewa, yarjejeniyar da Sin da Amurka suka kulla za ta inganta tattalin arzikin yankunan kasar Sin da na kasar Amurka, har ma da tattalin arziki na kasa da kasa baki daya.
David Paul Goldman, masanin tattalin arzikin kasar Amurka ya ce, kulla yarjejeniyar tattalin arziki da kasuwanci a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka a mataki na farko za ta sassauta sabanin cinikin dake tsakanin kasashen biyu, baya ga tallafawa kasashen Sin da Amurka, za kuma ta inganta bunkasuwar tattalin arzikin kasa da kasa. Ya ce,"Ina ganin kalubaloli za su ragu, kana harkokin zuba jari za su kyautata. Ya sa ake ganin da alamun, harkokin masana'antun kasar Amurka za su farfado. Lamarin na da muhimmanci ga kasashen da suke dogaro kan fitar da kayayyakinsu zuwa ketare, kamar kasar Jamus, da kasar Japan, da kuma kasar Koriya ta Kudu."
Shugaban kwamitin kasuwanci a tsakanin Sin da Amurka Craig Allen ya bayyana cewa, ba kawai yarjejeniyar za ta tallafawa al'ummomin kasashen Sin da Amurka, har ma za ta taimakawa bunkasuwar kasa da kasa. Ya ce, "Muna farin ciki sosai da kulla yarjejeniyar tattalin arziki da kasuwanci a tsakanin Sin da Amurka a mataki na farko, sabo da tana da mihimmiyar ma'ana ga kasar Sin da ma kasar Amurka. Tabbas, kasashen biyu za su ci gajiyar wannan yarjejeniya."
A nasa bangare, babban masanin tattalin arziki na kamfanin JP Morgan na kasar Amurka, Bruce Kasman ya ce, yarjejeniyar da kasar Amurka da Sin suka kulla ta samar da yanayi mai kyau ga bunkasuwar tattalin arzikin kasa da kasa cikin shekarar 2020. Ya ce, "A ganina, lamarin zai samar mana da yanayi mai kyau wajen tafiyar harkokin kasuwanci, musamman ma a lokacin da muke hasashen bunkasuwar tattalin arzikin duniya a shekarar 2020, sabo da yarjejeniyar ta rage damuwa da kalubaloli da muke fuskanta a fannin tattalin arziki da kasuwanci."
Haka kuma, shugaban kwamitin kasuwanci a tsakanin Sin da Amurka Craig Allen ya ce, yarjejeniyar da Sin da Amurka suka kulla za ta yi tasiri ga kasashen biyu kan fannonin ikon mallakar fasaha, da hada-hadar kudi, da ayyukan gona da dai sauransu, kuma za ta kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka. Ya ce, "Yarjejeniyar ta samar mana wani dandali, inda za mu iya kulla wata hulda mai karfi da samun dauwamammen ci gaba a tsakanin Sin da Amurka ta fuskar tattalin arziki da kasuwanci."
Shugaban yankin Brooklyn na birnin New York Eric Adams yana ganin cewa, yarjejeniya matakin farko ita ce matakin farko na farfado da dangantakar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka. ya ce, "Lokacin da za a dakatar da sabanin ciniki a tsakanin Sin da Amurka, zai kasance lokaci na cimma moriyar juna ga Sin da Amurka. Idan aka ci gaba da fuskantar sabanin cinikin tsakanin kasashen biyu, tabbas ba wanda zai cimma nasara. Ina da imanin cewa, dukkanin al'ummomin Sin da Amurka suna fatan dakatar da wannan sabani gaba daya. Za mu iya sake kasance abokan ciniki na kwarai a nan gaba."
Shugaban kwamitin kasuwanci a tsakanin Sin da Amurka Craig Allen ya kuma kara da cewa, kwamitin zai dukufa wajen ciyar da yarjejeniyar gaba, domin kyakkyawar dangataka a tsakanin kasashen Sin da Amurka za ta ba da taimako ga bunkasuwar kasashen biyu, da ma duniya baki daya. Ya ce, "A halin yanzu, mun shiga cikin sabbin shekaru 10, ina fatan za mu shiga cikin lokacin farfadowa bayan wannan babbar matsala da aka gamu da ita. Muna bukatar yin hadin gwiwa da cimma moriyar juna, ba kawai domin tallafawa al'ummomin kasashen biyu, har ma da duniya baki daya." (Maryam Yang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China