Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Yarjejeniyar ciniki a mataki na farko da Sin da Amurka suka kulla za ta taimaka wajen karawa kasuwannin kwarin gwiwa
2020-01-17 10:28:00        cri

Shugaban sashin kula da tsare-tsaren kudi na babban bankin jama'ar kasar Sin Sun Guofeng ya bayyana a jiya Alhamis a nan birnin Beijing cewa, yadda darajar kudin Sin RMB ta dan karu a kwanan baya na da alaka da yarjejeniyar ciniki a mataki na farko da Sin da Amurka suka kulla, yarjejeniyar za ta amfanawa Sin da kuma Amurka da ma duniya baki daya, kuma za ta karawa kasuwannin Sin da ma duniya kwarin gwiwa. Ban da wannan kuma, kasuwannin musanyar kudade da sauran kasuwannin hada-hadar kudi sun mai da martani mai yakini. An ce, tasiri mai kyau da yarjejeniyar ta haifar zai ci gaba.

Sun Guofeng ya yi wannan tsokaci ne yayin da taron manema labarai da bankin ya shirya a wannan rana, ya ce, kwan gaba kwan bayan musanyar kudaden Sin ya kai kimanin kashi 4 cikin dari a shekarar 2019, adadin da ya yi dai-dai a duniya. Kwan gaba kwan bayan musanyar kudade na daidaita tattalin arziki daga manyan fannoni da ba da tabbaci ga samun daidaito a harkokin cinikayyar duniya, kana matakin ya kara karfin tattalin arziki cikin gidan kasar Sin na tinkarar kalubaloli daga ketare. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China