Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ba ta ji dadin matakin Birtaniya da Faransa da Jamus na kaddamar da sabon tsarin cimma matsaya game da yarjejeniyar nukiliyar Iran ba
2020-01-15 21:05:25        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Geng Shuang, ya ce kasar sa ba ta ji dadin matakin da kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus suka dauka ba, na kaddamar da sabon tsarin cimma matsaya game da cikakkiyar yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran.

Geng Shuang wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudana a Larabar nan, ya ce Sin ba ta gamsu cewa, matakin kasashen na Turai zai iya kaiwa ga warware wannan matsala ba.

Rahotanni dai sun bayyana cewa, kasashen 3 sun aike da wasikar hadin gwiwa, ga babban wakilin kungiyar tarayyar Turai mai lura da manufofin harkokin waje da tsaro Josep Borrell, kafin daga bisani su fitar da sanarwar hadin gwiwa, inda suka bayyana kadamar da sabon salon da suka ce za su bi, wajen warware takaddamar da ta mamaye yarjejeniyar nukiliyar kasar ta Iran, suna masu cewa burin su shi ne ingiza yunkurin da ake yi, na ganin cewa Iran din ta aiwatar da wannan yarjejeniya.

Game da hakan, Geng Shuang ya ce har kullum ra'ayin Sin shi ne, Iran na da dalilan ta na ja da baya game da aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma kan nukiliyar ta. Kuma janyewar Amurka bisa radin kan ta, daga waccan yarjejeniya, shi ne tushen ja da baya da Iran din ta yi daga aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata.

Ya ce matakin Amurka ya sabawa dokokin kasa da kasa, wanda hakan ne kuma ya sanya Iran din jingine nauyin dake wuyan ta, tare da sanyaya gwiwar sauran sassa da batun ya shafa.

Geng Shuang ya jaddada cewa, a irin wannan yanayi da ake ciki yanzu, Sin na fatan dukkanin sassa za su kai zuciya nesa, su kuma rungumi tsarin aikin da kwamitin hadin gwiwa na aiwatar da waccan yarjejeniya ya tsara, su warware sabanin dake tsakanin su ta hanyar tattaunawa, da tuntubar juna, kana su martaba, da aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar da aka cimma yadda ya kamata. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China