Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iran ta ce ita ta kakkabo jirgin kasar Ukraine bisa kuskure
2020-01-11 15:43:22        cri
Rahoton gidan talabijin na Iran, ya ruwaito rundunar sojin kasar na cewa, ita ta kakkabo jirgin kasar Ukraine bisa kuskure, wanda ya yi sanadin mutuwar fasinjoji da ma'aikatan jirgin 176 a ranar Laraba.

A cewar gidan talabijin din, dakarun Iran sun dauki jirgin Ukraine din ne a matsayin na 'yan adawa bisa kuskure.

Shugaban Iran Hassan Rouhani, ya wallafa a shafinsa na Tweeter cewa, Iran ta yi matukar takaici da nadamar wannan mummunan kuskure, yana mai jajanta aukuwar lamarin

Ya kuma kara da cewa, Iran za ta ci gaba da bincike domin ganowa da hukunta wadanda suka yi mummunan kuskuren.

Shi kuwa ministan harkokin wajen kasar, Mohammad Javad Zarif, bayyana lamarin ya yi a matsayin ajizancin dan Adam, wanda rikicin da Amurka ta haifar ta yi sanadin aukuwarsa.

Jirgin saman fasinjan kasar Ukraine, ya fadi ne da safiyar ranar Laraba a kusa da filin jirgin saman Imam Khomeini dake Tehran, jim kadan bayan tashinsa.

Iran ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki da su bada gudunmawa wajen gudanar da bincike kan faduwar jirgin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China