Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Iran ta ce babu wani makami mai linzami da ya daki jirgin Ukraine kafin ya fadi
2020-01-10 19:49:17        cri
Shugaban hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Iran Ali Abedzadeh, ya yi watsi da rahotanni dake cewa, wani makami mai linzami ne ya daki jirgin saman fajinsan kasar Ukraine a sararin saman Tehran a ranar Laraba.

Ya shaidawa manema labarai cewa, "Mun yi imani cewa, babu wani makami mai linzami da ya daki jirgin saman Ukraine". Jirgin ya kama da wuta ne bayan dakika 90 da tashinsa. Haka kuma inda jirgin ya nufa da ma wurin da hadarin ya faru, sun nuna cewa, matukin jirgin ya yi kokarin dawowa filin jirgin saman.

Jami'in ya ce, ba masana ba ne suka yi bayani game da zargin da wasu ke yi na kaiwa jirgin hari da makami mai linzami, inda ya karyata ikirarin da jami'an kasashen Amurka da Canada ke yi game da yiwuwar harbo jirgin da makami mai linzami. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China