Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalisar dattawan Amurka ta zartas da daftarin takaita ikon shugaba na daukar makatan soja kan Iran
2020-02-14 15:19:28        cri
Majalisar dattawa ta Amurka ta zartas da wani daftari a jiya Alhamis, da zummar takaita ikon shugaban kasar, kan daukar matakan soja kan Iran.

A wannan rana, majalisar ta kada kuri kan wannan daftari, inda 'yan majalisa 55 suka amince, yayin da 45 suka kada kuri'ar kin amincewa. Daga cikinsu, mambobin jam'iyyar Republic 8 sun bayyana amincewarsu kan lamari. Daftarin ya bukaci shugaba da kada ya daukar matakan soja kan Iran ba tare da samun izni majalisar dokoki ba.

'Yan jam'iyyar Republic da suka amince da daftari sun nuna cewa, ba su da bambancin ra'ayi da shugaban, a maimakon haka, ana sa ran maido da ikon majalisar na yanke shawara kan matakan soja da za a dauka, ikon da ya dade da kubcewa majalisar dattawa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China