Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iran ta yi barazanar janyewa daga yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya
2020-01-21 13:40:11        cri
Kafar yada labarai ta kasar Iran ta bada labari a jiya Litinin cewa, ministan harkokin wajen kasar Mohammad Javad Zarif ya bayyana a wannan rana cewa, idan kasashen Turai sun mika batun nukiliyar Iran ga kwamitin sulhu na MDD, to Iran zata janye jikinta daga yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya.

A cewarsa, idan kasashen Turai sun iya sauke nauyin dake wuyansu game da wannan yarjejeniya, tare da bada tabbaci ga muradun tattalin arzikin Iran bisa tsarin yarjejeniyar, to Iran zata koma cikin wannan yarjejeniya. Ban da wannan kuma, Zarif ya ce, Birtaniya da Faransa da kuma Jamus sun fara aiki da tsarin daidaita bambancin ra'ayi kan yarjejeniyar, "ba bisa doka ba".

An bada labari cewa, Zarif ya yi wannan tsokaci ne don maida martani ga sabon matakin da wadannan kasashen uku suka dauka kan yarjejeniyar a makon da ya gabata. An ce a ranar 14 ga wata, wadannan kasashen uku sun sanar da amfani da tsarin daidaita bambancin ra'ayi kan yarjejeniyar don tinkarar yin watsi da yarjejeniyar da Iran ta yi. Idan kasashen uku sun yi amfani da wannan tsari, to ya yiwu za a mika batun Iran ga kwamitin sulhu na MDD. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China