Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Birtaniya da Jamus sun nemi kare yarjejeniyar nukiliya ta kasar Iran
2020-01-13 10:31:59        cri

Firaminisan kasar Birtaniya Boris Johnson da shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel sun bayyana a jiya Lahadi cewa, kasashensu za su tsaya kan alkawarinsu na kare matsayin yarjejeniyar batun nukiliyar kasar Iran.

Wani kakakin fadar firaministan kasar Birtaniya ya ce, shugabannin 2 na Birtaniya da Jamus sun tattauna ta wayar tarho, game da wasu batutuwan kasa da kasa. Game da yanayin kasar Libya kuwa, shugabannin 2 sun nanata bukatar neman sasanta yanayin da ake ciki ta hanyar shawarwari, tare da nuna goyon bayansu ga shirin daidaita al'amura a kasar, karkashin jagorancin MDD. Ban da haka, shugabannin 2 sun kuma tattauna batun harbo jirgin saman fasinja na kasar Ukraine.

Tun daga watan Yulin shekarar 2015, kasar Iran ta daddale yarjejeniyar batun nukiliya da kasashen Amurka, Birtaniya, Faransa, Rasha, Sin da kuma Jamus, inda suka amince cewa, kasar Iran za ta takaita shirinta na raya fasahar nukiliya, yayin da gamayyar kasa da kasa za su soke takunkumin da suka sanya mata. Sai dai kasar Amurka ta janye jiki daga yarjejeniyar a shekarar 2018, lamarin da ya sa Iran ta fara dakatar da aiwatar da yarjejeniyar a shekarar 2019. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China