Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nijeriya ta tsaurara matakan kandagarkin COVID-19 a filayen jiragen sama biyo bayan tabbatar da bullar cutar a kasar
2020-03-02 10:19:47        cri
Gwamnatin Nijeriya ta ce tana aiki da dukkan masu ruwa da tsaki wajen inganta daukar matakai dangane da kandagarkin cutar COVID-19 a filayen jiragen saman kasar.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasar, Musa Nuhu ya fitar, inda ya ce ana daukar matakan ne domin kare yaduwar cutar, biyo bayan tabbatar da samun wani dan kasar Italiya mai dauke da ita da ya sauka a kasar ta filin jirgin saman Murtala Muhammad dake jihar Lagos.

Musa Nuhu ya ce matakan kariya da aka dauka na da nufin tabbatar da an binciki lafiyar dukkan matafiyan dake shiga kasar.

Ya kuma shawarci kamfanonin jiragen sama da ma'aikatan filayen jiragen sama da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki, su dauki dukkan matakan da suka kamata na kare ma'aikatansu.

Har ila yau, ya shawarci matafiya da su kwantar da hankalinsu amma kuma su yi takatsantsa da daukar matakan da suka kamata wajen kare kansu yayin da suke bulaguro. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China