Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNICEF ta bayar da karin tallafin kayayyaki ga kasar Sin don yaki da cutar COVID-19
2020-03-02 10:20:52        cri
Asusun tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF) ya bayar da taimakon kayayyakin kiwon lafiya sama da ton 12 a gudunmowa ta baya bayan nan da ya aika yankin Shanghai a ranar Lahadi domin taimakawa kasar Sin a yaki da cutar numfashi ta COVID-19 da ta barke.

Kayayyakin sun hada da abun rufe fuska, da rigunan bada kariya, da gilashin rufe fuska, da safar hannu, da na'urar gwada yanayin zafin jiki, da kwalaben daukar jini, da sinadaren kashe kwayoyin cuta, kayayyakin dai za'a mika su ne zuwa lardin Hubei, inda cutar tafi kamari, kamar yadda hukumar ta sanar.

UNICEF ta fadawa manema labarai cewa, kayayyakin da ta bayar na baya bayan nan ya kai darajar dala miliyan 1, kuma nauyinsa ya zarce ton 30.

Kashin farko na kayayyakin da hukumar UNICEF ta bayar ya isa birnin Wuhan tun a ranar 30 ga watan Janairu, inda ta sake aikewa da wasu kayayyakin zuwa Beijing. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China