Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 2,837 sun warke daga cutar COVID-19 a babban yankin kasar Sin a ranar 1 ga watan Maris
2020-03-02 10:17:07        cri
Hukumar lafiyar kasar Sin ta sanar cewa baki daya mutane 44,462 aka sallama daga asibiti bayan sun warke daga cutar numfashi ta (COVID-19) a babban yankin kasar ya zuwa ranar Lahadin da ta gabata.

A rahoton da hukumar lafiyar kasar Sin ke sanarwar a kullum, a ranar ta Lahadi, mutane 2,837 aka sallama daga asibiti bayan sun warke daga cutar.

Ya zuwa karshen ranar Lahadi baki dayan adadin mutanen da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a babban yankin kasar Sin ya kai 80,026, yayin da mutane 2,912 ne cutar ta hallaka.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China