Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mai dauke da cutar COVID-19 a Najeriya na murmurewa
2020-03-02 10:18:27        cri
Kwamishinan lafiya na jihar Lagos a kudancin Najeriya Akin Abayomi, ya ce baturen kasar Italiyan nan dake dauke da cutar COVID-19, wanda yanzu haka ke samun kulawar musamman a jihar ya fara murmurewa.

Mr. Abayomi ya ce mutumin, wanda ya shiga Najeriya daga birnin Milan na kasar Italiya, bai nuna wasu sabbin alamu na rashin lafiya ba. Don haka ya yi kira ga al'umma da su kaucewa yada jita jita maras tushe, game da halin da ake ciki don gane da cutar ta Coronavirus, duba da yadda gwamnati ke daukar matakan kare lafiyar al'umma yadda ya kamata.

Kwamishinan ya kuma kara da cewa, nan da kwanaki 2 zuwa 3 masu zuwa, za a sake yiwa mutumin wasu karin gwaje gwaje, domin tabbatar da cewa babu sauran wasu kwayoyin cutar cikin yawun bakin sa. Kaza lika akwai fatan sallamar sa daga wurin da aka killace shi, da zarar an tabbatar ba ya dauke da kwayoyin cutar.

Daga nan sai kwamishinan ya jaddada cewa, gwamnatin Najeriya ta shirya tsaf, za kuma ta ci gaba da aiwatar da matakan dakile yaduwar cutar, ta hanyar matakai daban daban na kare lafiyar 'yan kasar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China