Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Syria ya ce fafutukar yakar son zuciya na yammacin duniya na ci gaba da gudana
2019-11-15 13:06:56        cri

Kamfanin dillancin labarai na SANA, ya ruwaito Shugaban Syria Bashar al-Assad a jiya na cewa, fafutukar yaki da son zuciya na yammacin duniya na ci gaba da gudana.

Bashar al-Assad ya bayyana haka ne yayin ganawarsa da Mojtaba Zonnouri, shugaban hukumar kula da tsaro da harkokin kasa da kasa nan a Iran, wanda ya kai ziyara birnin Damascus a ranar Alhamis.

Shugaban na Syria ya jaddada cewa kasar za ta ci gaba da yaki da zalamar kasashen yamma ta hanyar farwa mayaka da jami'ansu, wadanda ake cin nasara kansu a wurare daban daban.

A nasa bangaren, Zonnouri ya ce Syria za ta yi nasara duk da wahalhalun da take fuskanta.

Tsawon lokacin da aka shafe ana yaki a Syria, Iran ce ta kasance babbar kawar gwamnatin Assad. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China