Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alkaluman kididdiga sun nuna yadda tattalin arzikin kasar Sin ke farfadowa
2020-02-28 13:45:51        cri
A yayin da kasar Sin ke ci gaba da dakile yaduwar annobar cutar COVID-19 a duk fadin kasar, ana himmantuwa wajen farfado da ayyuka a sassa daban-daban na kasar. Wasu alkaluman kididdigar da aka fitar sun nuna yadda tattalin arzikin kasar ke farfadowa.

Tun daga ranar 10 ga wata, ban da lardin Hubei, wato inda cutar ta fi kamari, an farfado da ayyukan kere-kere sannu a hankali a sauran wuraren kasar, musamman lardunan Fujian da Jilin da Shanxi da Shandong da kuma birnin Tianjin, inda adadin mutanen da suka koma bakin ayyukansu ya zarce kaso 25.

Har wa yau, bisa kididdigar da kwamitin neman bunkasuwa da yin gyare-gyare na kasar Sin ya bayar, daukacin masana'antun samar da abun rufe baki da hanci sun farfado da ayyukansu na samar da wadannan kayayyakin rigakafin kamuwa da cutar. Kuma ma'aikatar kasuwancin kasar ta ce, zuwa karshen watan nan, kamfanonin kasashen waje a sassa da dama na kasar Sin sun riga sun farfado da ayyukansu.

Duba da yadda ake kokarin farfado da ayyukan kere-kere, gami da komawar ma'aikata bakin ayyukansu, tattalin arzikin kasar Sin na farfadowa yadda ya kamata.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China